Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 21:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ya jama'ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka, na faɗa muku abin da na ji daga Ubangiji Maɗaukaki, daga Allah na Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 21:10
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”


“Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka! Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe, kofatanki kuwa tagulla, Za ki ragargaje al'ummai da yawa.” Za ki ba Ubangijin dukan duniya dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya.


Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”


Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.


Ka ratsa duniya da hasala, Ka kuma tattake al'umman duniya da fushi.


Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”


Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”


Ba zai yi ta bugun alkama, har ya ɓata tsabar ba, ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


Zaki ya yi ruri! Wa ba zai ji tsoro ba? Sa'ad da Ubangiji ya yi magana! Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ