Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 21:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Wannan shi ne jawabi a kan Babila. Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku. Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu, mai hari ya zo daga hamada, daga ƙasar mai banrazana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 21:1
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”


Teku ta malalo a kan Babila, Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta.


Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.


Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su, Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya, Ubangiji Allah zai busa ƙaho, Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.


Wannan shi ne jawabi a kan Dimashƙu. Ubangiji ye ce, “Dimashƙu ba za ta ƙara zama birni ba, za ta zama tsibin kufai ne kawai.


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.


Shi da mutanensa, Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma, Za a kawo su don su hallakar da ƙasar. Za su zare takubansu a kan Masar, Su cika ƙasar da gawawwaki.


Guguwa takan taso daga inda take, Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.


Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.


Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.


Za ka ci gaba, kana zuwa kamar hadiri, za ka rufe ƙasar kamar gizagizai, kai da rundunarka, da jama'a masu yawa tare da kai.’ ”


Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.


Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.


Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka.


Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!


Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan kawo iskar ɓarna a kan Babila Da mazaunan Kaldiya.


Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ