A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.
Zan shafe mutum da dabba, Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.
Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”
Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.
Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.
Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”
Ubangiji Allah ya ce, “Zan hallakar da gumaka Da siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba, Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.
Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.”
A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.
Ubangiji zai tsananta musu, Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa. Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake, Har da ƙasar sauran al'umma.