Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.
Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.
Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.