Ishaya 19:21 - Littafi Mai Tsarki21 Ubangiji zai bayyana kansa ga mutanen Masar, sa'ad da ya yi haka kuwa, za su karɓe shi, su yi masa sujada, su kuma kawo masa hadayu da sadakoki. Za su yi masa alkawarai ƙwarara, su kuwa cika abin da suka alkawarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.