Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa'an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.
Ubangiji kuma ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa ya miƙa shi a bisa ruwayen Masar, da kogunansu, da rafuffukansu, da fadamunsu, da dukan tafkunansu don ruwansu ya zama jini. Jini zai kasance ko'ina a ƙasar Masar, i, har ma cikin randuna.