Ishaya 18:7 - Littafi Mai Tsarki7 A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al'umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al'ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya.