Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 17:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Amma ko da za su toho su yi fure a safiyar da kuka dasa su, duk da haka ba za a girbe kome ba. Wahala ce kaɗai da azabar da ba ta warkuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 17:11
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama sun shuka iska Don haka zu su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya, Ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,


Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta, Suna shuka mugunta, Suka kuwa girbe mugunta.


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


An ka da mutanen Ifraimu, saiwarsu ta bushe. Ba za su yi 'ya'ya ba. Ko ma sun haihu, zan kashe 'ya'yan nan nasu waɗanda suke ƙauna.”


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Su yi girma har su yi huda, Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.


Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.


Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.


Isra'ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa'ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu.


Itatuwa sun mutu a busasshiyar ƙasa, Ba hatsin da za a adana a rumbu, Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ