Ishaya 16:7 - Littafi Mai Tsarki7 Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.