Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
Yanzu Ubangiji ya ce, “A shekara uku daidai, dukiyar Mowab mai yawan nan za ta ƙare. Daga cikin ɗumbun mutanenta 'yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”