Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu, Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi. Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al'ummar Da ta zalunci jama'arka, ta kuma zambace su, Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.
Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama!
Ubangiji ya ce, “Zan kawo masifa a duniya. Zan hukunta dukan mugaye saboda zunubansu. Zan ƙasƙantar da kowane mai girmankai. Zan hukunta kowane mai izgili da mai mugunta.
“Sun ji yadda nake nishi, Ba mai ta'azantar da ni. Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki, Suna kuwa murna da ka yi haka. Ka kawo ranan nan da ka ambata, Domin su ma su zama kamar yadda nake.
Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji, Ka sa su yi farin ciki. Suna murna da abin da ka aikata, Kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke girbin hatsi, Ko sa'ad da suke raba ganima.