Ishaya 14:20 - Littafi Mai Tsarki20 Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.