Sa'ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.
Sa'an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha'awar mace. Daga nan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.
Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi.
amma kai ba ka sami kabari ba, jefar da gawarka aka yi don ta ruɓe. Aka hautsuna gawarka da gawawwakin mayaƙan da aka kashe cikin yaƙi. Tare da su aka jefa ka gangaren dutse, aka tattake.