Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.
Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
Al'ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa'ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta'azantu a lahira.
An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”
Girmankanki ya yaudare ki, Kina zaune a kagara, a kan dutse, Wurin zamanki yana can ƙwanƙolin duwatsu. Don haka a zuciya kike cewa, ‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’