“Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya. Kin ɗauka kina da girma kamar Allah, Har kina ganin ba wani kamarki. Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba, Ko ki sha hasarar 'ya'yanki.
Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.
“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.
Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!
“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.