Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 14:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 14:13
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.


Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.


“Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar, Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna, Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.


Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.


Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.


Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce, “ ‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!


A kwanaki masu zuwa, Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka. Al'ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.


Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo, Mai kyan gani ne na Allah, Birnin babban Sarki. Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!


Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?


Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.


Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama. Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.


Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da yake kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”


“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,


A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.


Girmankanki ya yaudare ki, Kina zaune a kagara, a kan dutse, Wurin zamanki yana can ƙwanƙolin duwatsu. Don haka a zuciya kike cewa, ‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ