Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 13:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ba wanda zai ƙara zama a cikinta. Ba wani Balaraben da yake yawo da zai kafa alfarwarsa a can. Ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 13:20
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Garuruwanta sun zama abin ƙyama, Ta zama hamada, inda ba ruwa, Ƙasar da ba mazauna, Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.


Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”


Duniya ta girgiza, tana makyarkyata saboda azaba, Gama nufin Ubangiji na gāba da Babila ya tabbata, Nufinsa na mai da ƙasar Babila kufai, inda ba kowa.


“Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai hallakarwa, Wanda ya hallaka duniya duka. Zan miƙa hannuna gāba da kai, Zan mirgino da ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, Zan maishe ka ƙonannen dutse.


Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango.


“Domin haka namomin jeji da diloli za su zauna a Babila, Haka kuma jiminai. Ba za a ƙara samun mazauna a cikinta ba har dukan zamanai.


“Ku haura ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da mazaunan Fekod. Ku kashe, ku hallaka su sarai, Ku aikata dukan abin da na umarce ku, Ni Ubangiji na faɗa.


Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta.


“Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”


Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700).


Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.


Faɗa mini, ƙaunataccena, Ina za ka kai garkenka kiwo? Ina za su huta sa'ad da rana ta take? Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?


Wannan shi ne jawabi a kan Babila. Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.


Hazor za ta zama kufai har abada, wurin zaman diloli, Ba wanda zai zauna a ciki, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”


Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.


Ka mai da birane kufai Ka lalatar da kagaransu, Wuraren da maƙiya suka gina kuwa, An shafe su har abada.


Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ