15 Duk wanda aka kama za a soke shi ya mutu.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
Ku kashe dukan bijimanta, a kai su mayanka! Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare, Lokacin hukuncinsu ya yi.
Ubangiji ya buɗe taskar makamansa, Ya fito da makaman hasalarsa, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana da aikin da zai yi a ƙasar Kaldiyawa.
Mutane suna gudu don su tsere wa takuban da za su kashe su, da bakkunan da za su harbe su, su kuma tsere wa dukan hatsarorin yaƙi.
Da kai ne na farfasa karusa da mahayinsa. Da kai ne na kakkarya mace da namiji, Da kai ne na kakkarya tsoho da saurayi, Da kai ne na kakkarya saurayi da budurwa,