Sa'ad da wannan lokaci ya yi, mata bakwai za su riƙe mutum guda su ce, “Mā iya ciyar da kanmu, mu kuma tufasar da kanmu, amma in ka yarda, bari mu ce kai ne mijinmu, domin kada mu sha kunyar zaman gwagwarci.”
Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna. A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye. Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.
Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.