Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 13:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Kowane tauraro, da kowace ƙungiyar taurari za su daina ba da haske. Rana za ta yi duhu lokacin da ta fito, wata kuwa ba zai ba da haske ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 13:10
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama.


“Amma lokacin nan, wato bayan tsabar wahalan nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba.


Rana za ta duhunta, Wata zai zama ja wur kamar jini, Kafin isowar babbar ranan nan mai bantsoro ta Ubangiji.


Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.


“Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.


Rana da wata sun yi duhu, Taurari kuma ba su haskakawa.


Sa'ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra'ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.


Duniya takan girgiza saboda ita, Sammai sukan yi rawar jiki. Rana da wata sukan duhunta, Taurari kuwa sukan daina haskakawa.


Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.


A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya.


Za a mai da rana duhu, Wata kuma jini, Kafin Ranar Ubangiji ta zo, Babbar ranar nan mai girma.


Allah yana da iko ya hana rana fitowa, Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.


Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa.


Ubangiji ya ce wa Babila, “Ki zauna shiru a cikin duhu, Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al'ummai ba!


Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu, In sa ya zama makoki domin matattu.”


Ranar Ubangiji za ta kawo baƙin ciki, Ba murna ba. Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.


Zai shafe maƙiyansa da ambaliyar ruwa, Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwa cikin duhu.


A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ