Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 12:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 12:3
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.


Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,


domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Mutanena sun yi zunubi iri biyu, Sun rabu da ni, ni da nake maɓuɓɓugar ruwan rai, Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa, hudaddu, Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.


Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba. Ba za su sha zafin rana da na hamada ba, Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su. Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.


Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.


Kai ne mafarin dukan rai, Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske.


Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji, Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza. Da farin ciki na zauna a inuwarsa, Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.


Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce, “Ubangiji ya cika zuciyata da murna. Ina farin ciki da abin da ya yi. Ina yi wa maƙiyana dariya, Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.


Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai, Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka. Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa, Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.


Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu.


Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa, Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”


“A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ