“Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba.
Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.
Ko da yake sun yi ijara da abokai daga cikin al'ummai, Yanzu zan tattara su, in hukunta su. Sa'an nan za su fara ragowa, Ta wurin tunanin nawayar Sarkin sarakuna.