Ishaya 10:33 - Littafi Mai Tsarki33 Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202033 Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.