Ishaya 10:20 - Littafi Mai Tsarki20 Lokaci zai yi sa'ad da jama'ar Isra'ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al'ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”