Ishaya 1:4 - Littafi Mai Tsarki4 An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.