Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 1:3
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko shamuwa ta sararin sama ma, ta san lokatanta, Tattabara da tsattsewa, da gauraka suna kiyaye lokacin komowarsu. Amma mutanena ba su san dokokina ba.’ ”


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.


A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.


Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.


Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka? Sai yaushe za ku koya?


Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.


Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.


Kowane mutum dakiki ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa, Gama siffofinsa ƙarya ne, Ba numfashi a cikinsu.


Dukansu dakikai ne wawaye, Koyarwar gumaka ba wani abu ba ne, itace ne kawai!


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.


Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.


“Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya.


Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.


“Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, Da azurfa, da zinariya da yawa Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.


Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.


Isra'ila, kun ga abu da yawa, Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan. Kuna da kunnuwan da za ku ji, Amma a ainihi me kuka ji?”


'Ya'yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama'an nan ba su yi mini biyayya ba.


“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ