Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,” “Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!” Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,” “Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”
Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.
Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.
Ubangiji ya ce wa jama'arsa, “Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba, Amma ga shi, kuka zama bayi. Ba za a biya kuɗin fansa domin a 'yantar da ku ba, Amma, ga shi, za a 'yantar da ku.
Ya ku jama'ata, ku tuna Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla, Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya amsa masa, Da abin da ya faru daga Shittim, har zuwa Gilgal, Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”