Ishaya 1:21 - Littafi Mai Tsarki21 Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!