Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 9:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Saboda haka, Ubangiji Mai Runduna, ya faɗa cewa, “Zan tsabtace su, in gwada su, Gama me zan yi kuma saboda jama'ata?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 9:7
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku.


Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa'an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace.


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Na maishe ka mai aunawa da mai jarraba mutanena Domin ka sani, ka auna al'amuransu,


Na gwada ku da wutar wahala, Kamar yadda ake tace azurfa a tanda, Amma na tarar ba ku da amfani.


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku.


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.


Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama'arsa da wurin zaman zatinsa.


Sa'an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan'uwana ya tafi tare da mu.” Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”


Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, Zai kuwa taimake ka, Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.


Ga Allah kaɗai na dogara, A gare shi na sa zuciyata.


Da kibau masu tsini na mayaƙa, Da garwashin wuta zai hukunta ku!


Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.


“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.


Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji, Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar. “Gama ba gaskiya, ko ƙauna, Ko sanin Ubangiji a ƙasar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ