Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 9:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kowane mutum yana ruɗin maƙwabcinsa da abokinsa, Ba mai faɗar gaskiya, Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya. Suna aikata laifi, Sun rafke, sun kasa tuba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 9:5
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba? Sun kuma gajiyar da kansu a banza?


Attajiran birnin sun cika zalunci, Mazaunansa kuwa maƙaryata ne, Harshensu na yaudara ne.


Kun damu saboda nisan hanyarku, amma ba ku ce, “Ba shi da wani amfani ba.” Ƙarfinku ya sake sabunta ranku, don haka ba ku suma ba.


Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu, Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.


ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas.


Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.


“Ya ku jama'ata, me na yi muku? Wace irin fitina nake yi muku? Ku amsa mini!


Ta gajiyar da ni a banza, Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.


Harshensu kibiya ce mai dafi, yana faɗar ƙarya, Kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa Amma a zuciyarsa yana shirya masa maƙarƙashiya.


Ubangiji ya ce, “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a ƙasar. Suna ta cin gaba da aikata mugunta, Ba su kuwa san ni ba.


Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.


Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani.


Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi, Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.


Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.


“Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta, Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.


Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa, Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi.


Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?


Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.


Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta, Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.


Za ka faɗa musu ka ce, wannan ita ce al'ummar da ba ta yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnta ba, ba ta karɓi horo ba. Gaskiya kuma ta ƙare sam, ba ta a bakinsu.


Gama har da 'yan'uwanka da gidan mahaifinka, Sun ci amanarka, Suna binka da kuka, Kada ka gaskata su, Ko da yake suna faɗa maka maganganu masu daɗi.”


Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”


Mutumin Habasha zai iya sāke launin fatar jikinsa? Ko kuwa damisa za ta iya sāke dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin nagarta, Ku da kuka saba da yin mugunta.


“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, Za a baje garun nan na Babila mai fāɗi Za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta. Mutane sun wahalar da kansu a banza. Sauran al'umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”


Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ” Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.


Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?


Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.


Amintattun mutane za su yi maka abin da yake daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ