Irmiya 9:4 - Littafi Mai Tsarki4 “Bari kowane mutum ya yi hankali da maƙwabcinsa, Kada kuma ya amince da kowane irin ɗan'uwa, Gama kowane ɗan'uwa munafuki ne, Kowane maƙwabci kuma mai kushe ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba, duban raini, harshe mai faɗar ƙarya, hannuwan da suke kashe marasa laifi, kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru, mutum mai gaggawar aikata mugunta, mai yawan shaidar zur, mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.