Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 9:26 - Littafi Mai Tsarki

26 da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 9:26
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu,


Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.


“Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.


“Za a washe raƙumansu da garkunan shanunsu ganima, Zan watsar da masu yin kwaskwas ko'ina, Zan kuma kawo musu masifu daga kowace fuska, Ni Ubangiji na faɗa.


Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.


Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta 'ya'yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu.


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Da wa zan yi magana don in faɗakar da shi, don su ji? Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su ji, Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta zama abin ba'a a gare su, Ba su marmarinta.


Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.


Haka kuma Yahudawan da suke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu,


“A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Ka ce, ‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ