Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.