Irmiya 9:20 - Littafi Mai Tsarki20 Irmiya ya ce, “Ya ku mata, ku ji maganar Ubangiji, Ku kasa kunne ga maganar da ya faɗa, Ku koya wa 'ya'yanku mata kukan makoki, Kowacce ta koya wa maƙwabciyarta waƙar makoki, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji; ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina. Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka; ku koya wa juna makoki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.