Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 8:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Na kula sosai, na saurara, Amma ba wanda ya faɗi wata maganar kirki, Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa, Kowa cewa yake, “Me na yi?” Kamar dokin da ya kutsa kai cikin fagen fama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 8:6
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane, Yă ga ko da akwai masu hikima Waɗanda suke yi masa sujada.


Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba.


Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.


Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.


Mutanen kirki sun ƙare a duniya, Ba nagarta a cikin mutane. Dukansu suna kwanto don su zub da jini. Kowa yana farautar ɗan'uwansa da tarko.


Sauran 'yan adam waɗanda bala'in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku lura da al'amuranku!


Yanzu, ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku lura da al'amuranku!


Sai na nemi mutum a cikinsu wanda zai gina garun ya tsaya a hauren garun a gabana, domin kada in hallaka ƙasar, amma ban sami kowa ba.


“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.


Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa'an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa.


Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.


Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.


Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’


“Akwai wanda zai ce wa Allah, ‘Ni horarre ne, Ba zan ƙara yin laifi ba?


Ka koya mini abin da ban sani ba, Idan na yi laifi, ba zan ƙara yi ba.’


Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.


Za ka dinga yin fushi da ni? Za ka husata da ni har abada?’ Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi, kin aikata dukan muguntar da kika iya yi.”


Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.


Na ce, hakika za ka ji tsorona, Ka kuma karɓi horo. Ba za a rushe wurin zamanta ba Bisa ga hukuncin da na yi mata. Amma suka ɗokanta su lalatar da ayyukansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ