Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 8:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ka saurari kukan mutanena daga ƙasa mai nisa suna cewa, “Ubangiji ba ya a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya can ne kuma?” “Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi, da baƙin gumakansu marasa amfani?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 8:19
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”


Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.


“Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.


“Amma za a sami waɗanda za su tsira daga Dutsen Sihiyona, Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki. Jama'ar Yakubu za ta mallaki mallakarta.


Zan sāka alhakin jininsu, Ba zan kuɓutar da mai laifi ba, Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”


Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda suke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.”


Gama rana tana zuwa sa'ad da mai tsaro zai yi kira A ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce, ‘Ku tashi mu haura zuwa Sihiyona Zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”


“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.


Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma! Birni mai tsarki na Allah, Ki yafa wa kanki jamali! Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.


Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama'a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu.


Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”


An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.


Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki, Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!


Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai! Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!


Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa. Ku yabi Ubangiji!


Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.


“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.


Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare ka.


Ubangiji ya ce, “Wane laifi ne na yi wa kakanninku, Da suka bar bina? Suka bauta wa gumaka marasa amfani, Su kuma suka zama marasa amfani.


In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”


Mutane suna ta cewa, “Damuna ta ƙare, kaka kuma ta wuce, Amma ba a cece mu ba.”


Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne, A lokacin da za a hukunta su za su lalace.


Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san abin da zai yi ba, Kamar jarumin da ya kasa yin ceto? Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan a tsakiyarmu. Da sunanka ake kiranmu, Kada ka bar mu!”


Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace.


Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.


Da'irar birnin kamu dubu goma sha takwas (18,000) ne. Daga wannan lokaci za a kira birnin, ‘Ubangiji Yana Nan!’ ”


Yanzu, me ya sa kike kuka da ƙarfi? Ba sarki a cikinki ne? Mashawarcinki ya hallaka ne, Da azaba ta auka miki kamar ta mace mai naƙuda?


A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’


A bakin kogunan Babila Muka zauna muka yi ta kuka, Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.


Ubangiji ya kawar miki da hukuncinsa, Ya kuma kori abokan gābanki. Ubangiji Sarkin Isra'ila, yana a tsakiyarki, Ba za ki ji tsoro ba.


Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ