Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.
A kan annabawa kuwa, zuciyata ta karai, Dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa, Saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki. Na zama kamar mashayi, wanda ya bugu da ruwan inabi,