Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.
Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”
Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu, Gonakinsu kuma ga waɗanda suke cinsu da yaƙi, Saboda tun daga ƙarami har zuwa babba Kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba, Tun daga annabawa zuwa firistoci Kowannensu aikata ha'inci yake yi.
Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama'an nan da Urushalima, da ka ce musu, ‘Za ku zauna lafiya,’ amma ga shi, takobi zai sassare su.”
Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.
Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.