Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 7:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Tun daga ran da kakanninku suka fito ƙasar Masar, har zuwa yau na yi ta aika musu da dukan bayina annabawa kowace rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 7:25
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da yake Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa,


Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama'arsa da wurin zaman zatinsa.


Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama'ar Isra'ila, al'umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau.


Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba,


“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.


“Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su, Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne. Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.


Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.


“Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.


Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’


Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.


Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi 'ya'yan inabi masu tsami, maimakon 'ya'yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.


Lokacin da na fito da kakanninsu daga ƙasar Masar na faɗakar da su musamman, na yi ta faɗakar da su har wannan rana, ina cewa, ‘Ku yi biyayya da maganata.’


“Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.


Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa.


Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa 'ya'yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba.


Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.


Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama.


“Na yi magana da annabawa, Ni ne na ba da wahayi da yawa, Da misalai kuma ta wurin annabawa.


Na zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yanku su zama annabawa, Waɗansu kuma daga cikin samarinku su zama keɓaɓɓu. Ko ba haka ba ne, ya ku Isra'ilawa? Ni, Ubangiji, na yi magana.


Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’


Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ