Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 7:12 - Littafi Mai Tsarki

12 “ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 “ ‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 7:12
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”


Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.


A kowace shekara Elkana yakan haura daga garinsu zuwa Shilo domin ya miƙa wa Ubangiji Mai Runduna hadaya, ya kuma yi masa sujada. 'Ya'yan Eli, maza biyu, Hofni da Finehas, su ne firistoci na Ubangiji a can.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.


domin haka zan yi wa Haikali wanda ake kira da sunana, wanda kuma kuka amince da shi, da kuma wurin da na ba ku, ku da kakanninku, kamar yadda na yi wa Shilo.


sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ