To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama'arsa baya ke nan? A'a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba'isra'ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.
“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.
“Kai Irmiya, sa'ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, ‘Mece ce nawayar Ubangiji?’ Sai ka ce masa, ‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,’ ni Ubangiji na faɗa.