Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 6:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Mutanen Urushalima sun ce, “Mun ji labarin yaƙin, Hannuwanmu suka yi rauni. Azaba ta kama mu, Ciwo irin na mai naƙuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas. Azaba ta kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 6:24
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.


Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi, Ta juya, ta gudu, Tsoro ya kama ta, Azaba da baƙin ciki sun kama ta kamar na naƙuda.


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Yanzu ku tambaya, ku ji, Namiji ya taɓa haihuwa? To, me ya sa nake ganin kowane namiji yana riƙe da kwankwaso, Kamar mace mai naƙuda, Fuskar kowa kuma ta yi yaushi?


Me za ku ce sa'ad da aka naɗa muku shugabanni, Waɗanda ku da kanku kuka koya musu, suka zama abokanku? Ashe, azabai ba za su auko muku ba Kamar yadda sukan auko wa mace mai naƙuda?


Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!


Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.


Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.


Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.


Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda suke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!


Tsoro ya kama su suka razana, Kamar mace wadda take gab da haihuwa.


Belshazzar sarki fa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune, fādawansa duk suka ruɗe.


Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.


Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ