Irmiya 6:21 - Littafi Mai Tsarki21 Don haka, ni Ubangiji na ce, Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan jama'a, Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi. Iyaye tare da 'ya'yansu, da maƙwabci, Do abokansu za su lalace.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’