Irmiya 6:20 - Littafi Mai Tsarki20 Da wane nufi kuke kawo mini turare daga Sheba, Ko raken da kuke kawowa daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba, Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinku ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.