Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 6:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Sun ji kunya sa'ad da suka aikata abubuwan banƙyama? Ba su ji kunya ba ko kaɗan. Ko gezau ba su yi ba, Don haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a hamɓarar da su. Ni Ubangiji na faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 6:15
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko sun ji kunya Sa'ad da suka aikata ayyuka masu banƙyama? A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan, Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba. Domin haka za su faɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a ci su da yaƙi. Ni Ubangiji na faɗa.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


Saboda haka aka ƙi yin ruwa, Ruwan bazara bai samu ba. Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jin kunya.


Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya.


Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne, Ba ya kuskure. Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba. Amma mugu bai san kunya ba.


Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake, Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen ƙaya yake. Ranar da kuka sa mai tsaro, A ran nan za a aukar muku da hukunci. Yanzu ruɗewarku ta zo,


Saboda haka kome zai zama dare da duhu, ba wahayi ko duba. Rana za ta fāɗi a kan annabawa, Yini zai zama musu duhu baƙi ƙirin.


Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso, Isra'ila za ta sani! An ce annabi wawa ne, Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne, Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.


Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta, Ta zubar da shi a kan dutse, Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.


Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.’


“Saboda haka hanyarsu za ta zama da santsi da duhu, Inda za a runtume su, su fāɗi. Gama zai kawo musu masifa a shekarar da za su sha hukuncinsu.” Ubangiji ya faɗa.


“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?


Ba zan hore su saboda waɗannan abubuwa ba? Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa kaina fansa a kan wannan al'umma ba?


Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.


Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.


Yanzu fa, sai ka tafi, ka bi da mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka, ga shi, mala'ikana zai wuce gabanka. Duk da haka a ranar da zan waiwaye ku, zan hukunta su saboda zunubinsu.”


Za a kunyatar da masu hikima. Za su tsorata, za a kuma tafi da su. Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji. Wace hikima suke da ita?


Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”


Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.


Zan rushe garun da kuka shafe da farar ƙasa. Za a baje shi, a bar tushen a fili. Za ku halaka a tsakiyarsa sa'ad da ya fāɗi, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.


Ya ke al'umma marar kunya, ku tattaru, ku yi taro,


A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.


Kashegari kuma, 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Ga shi, daren jiya na kwana da mahaifina, bari daren yau kuma, mu sa shi ya sha ruwan inabi, ke ma sai ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”


Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.


Za ku yi tuntuɓe da rana, Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare, Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ