Irmiya 52:8 - Littafi Mai Tsarki8 Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’