Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 52:30 - Littafi Mai Tsarki

30 A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba'in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4,600).

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745. Jimillarsu duka 4,600 ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 52:30
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Za a kalace ringin Isra'ila sarai, kamar yadda ake wa inabi, Ka miƙa hannunka a kan rassanta kamar mai tsinkar 'ya'yan inabi.”


A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.


Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.


Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.


A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ