Irmiya 52:18 - Littafi Mai Tsarki18 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar Haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi. ginshiƙai biyu dajiya da take a kawunan ginshiƙan raga biyu don rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙai siffofin rumman ɗari huɗu domin raga biyu ɗin, da jeri biyu na siffofin rumman domin kowace raga don a rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙan dakalai goma daruna goma a kan dakalan kwatarniya ɗaya siffofin bijimai guda goma sha biyu da kwatarniya take zaune a kai, tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da kwanoni. Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya. Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.