Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 52:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 52:15
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.


Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.


Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.


Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’


da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ