Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 51:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Mun ba Babila magani, amma ba ta warke ba. Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya koma garinsu, Gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo har samaniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “ ‘Da mun warkar da Babilon, amma ba za tă warke ba; mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu, gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo kamar gizagizai.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 51:9
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama, Allah kuwa ya tuna da laifofinta.


Ku datse wa Babila mai shuka, Da mai yanka da lauje a lokacin girbi. Saboda takobin azzalumi, Kowa zai koma wurin mutanensa, Kowa kuma zai gudu zuwa ƙasarsa.”


“Baƙin da yake zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi.


Sun yi ta fāɗuwa, Suna faɗuwa a kan juna, Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma wurin mutanenmu, Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu daga takobin azzalumi!’


Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.


Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa ne, masu yawan kitse, Sun ba da baya, sun gudu, ba su tsaya ba, Domin ranar masifarsu ta zo, Lokacin halakarsu ya yi.


Mutane suna ta cewa, “Damuna ta ƙare, kaka kuma ta wuce, Amma ba a cece mu ba.”


Nan ne inda shawararsu za ta kai ki, Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki. Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa, Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”


Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.


Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata, Kada zunubanta su shafe ku, Kada bala'inta ya taɓa ku.


“Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni. Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini. Ko da yake zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ